Wani gungun masu zanga-zanga ya sanya wuta a wasu sassan gonar iyalan tsohon shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta a abin da ake gani kamar wani martini ne ga mummunar zanga-zangar da ‘yan hamayya ke yi.
Wakilin BBC da ya kasance a gonar lokacin da masu zanga-zangar suka far mata, a wajen babban birnin kasar Nairobi ya ce ya ga yadda mutanen ke da kwasar tumakai inda wani ya ce zai sayar da wadda ya dauka dala 23.
Babu ‘yan sanda a wurin kuma wasu daga cikin masu zanga-zangar na dauke da adduna, inda suka rika sare bishiyoyi da sauran shuke-shuke, bayan sun kori ma’aikatan da suka tarar a gonar.
Masu harkokin kasuwanci da ke kusa da gonar da kuma wadanda suke tsakiyar birnin na Nairobi sun rurrufe.