fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Masu zanga zanga sunyi arangama da jami’an yan sanda inda suka jikkata jami’ai 5 a jihar legas

Lamarin ya faru ne a jihar legas inda wasu ma’aikata a matatar man Dangote da kuma masu aiki a tashar shigar da kayayyaki daga kasashen waje sun yi arangama da jami’an ‘yan sanda lokacin da suka nemi rufe wuraren da suke aiki a unguwar Lekki.

 

Wasu da suka shaida aukuwar lamarin sun ce, fadan ya kaure ne a lokacin da wasu matasa suka cinnawa tayoyi wuta akan tituna, tare da zargin jami’an tsaro da fifita wani bangare yayin tilasta bin dokar hana fitar dake aiki a unguwar at Lekki, don dakile yaduwar annobar coronavirus.

Karanta wannan  An kama 'yansandan boge 5 a jihar Nasarawa

 

Kakakin ‘yan sandan jihar ta Legas Bala Elkana, yace masu zanga-zangar sun raunata jami’ansu guda 5, yayinda su kuma suka kama 51 daga cikin su.

 

 

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.