Masu zanga-zangar SARS a yanzu sun canja akala inda suka fitar da sabbin bukatu 7. Dsga cikin bukatun da suke da suke dasu sune a saka dokar ta baci a bangaren Ilimi da kiwon lafiya.
Sun kuma bukaci canja kundin tsarin mulki yanda za’a saka matasa a ciki, sannan sun bukaci a rage yawan kudin da ake kashewa ma’aikatan gwamnati, musamman majalisar tarayya inda suka bukaci a mayar da zamanta na wucin gadi.
Sun bukaci duk wani me rike da mukamin gwamnati ya mayar da dansa makarantar gwamnati sannan ya koma amfani da Asibitin gwamnati ko kuma ya sauka idan ba zai iya ba.
Sannan a cire kariyar da doka ta baiwa shuwagabanni wadda ta basu kariyar shiga Kotu, duk wanda ake zargin aikata ba daidai ba a kaishi kotu kuma idan an sameshi da laifi ya sauka.
Sannan ‘yansanda dole a samar musu gidaje masu kyau, a kyautata Albashinsu da samar musu inshorar rayuwa yayin da suke aiki da bayan sun bar aikin sannan a basu kayan aiki na zamani.





Wannan gaskiyane muna bayanku bukatunku sunyi babu na gefarwa