fbpx
Thursday, September 29
Shadow

Masu zolayar Tinubu kan shekarunsa ba lalle ku kai lokacin da zaku ga tsufar ku ba, cewar jarumin Nollywood

Jarumin masana’antar Nollywood Yul Edochie ya caccaki mutanen dake zolayar Tinubu kan shekaraunsa da kuma rashin lafiyarsa.

Inda ya bayyana cewa ita rashin lafiya Allah na iya dorawa kowa ita babba da kuma yaro, sannan it kuma tsufa kyautace daga Allah bama kowa ne yake kaiwa lokacin ba.

Saboda haka yace abinda ake yiwa Tinubu bai kamata ba kawai idan mutun bai son shi to shikenan amma ba wai ya rika zolayarsa ba.

Yawancin al’ummar kasar nan musamman mabiya jam’iyyar hammayar APC suna zolayar dan takarar shugaban kasar nata kan shekarunsa da kuma lafiyarsa.

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published.