fbpx
Sunday, February 28
Shadow

Mata masu tallar nono ke yi wa ƴan fashi fataucin ƙwayoyi>>Gwamna Tambuwal

Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya ce wani gwamna ya ba shi labarin cewa mata masu tallar nono suna fakewa da sana’ar domin safarar ƙwayoyi ga ƴan bindiga masu satar mutane.

Gwamnan ya ce yawancin ƴan bindiga masu satar mutane na samun ƙwayoyi ne ta hanyar masu tallar nono, kamar yadda takwaransa gwamnan wata jiha ya shaida masa.

Gwamnan ya faɗi haka ne a lokacin ya karɓi baƙuncin Sheikh Ahmad Gumi a Sokoto a ranar Lahadi a ci gaba da da’awar da malamin addinin ke yi na yunƙurin sasanci da ƴan fashin daji masu garkuwa da mutane.

Duk da bai ambaci sunan gwamnan ba, amma a sanarwar da kakakinsa ya fitar Muhammad Bello, Gwamna Tambuwal ya bayar da labarin abin da takwaransa ya faɗa masa a ganawarsa da Sheikh Gumi.

“Wata rana ya taba kiran wata mai tallar nono amma ta gudu, bayan ya tambayi dalili sai aka faɗa masa cewa ba nono ba ne ƙwayoyi ne cikin ƙwaryarta.”

“Saboda wannan dalili, dole ne mu ɗauki mataki don shawo kan wannan matsalar ta fatauci da kuma shan muggan kwayoyi, idan ba haka ba, kamar mun kashe maciji ne ba tare da yanke kan sa ba,” in ji shi.

Sokoto na ɗaya daga cikin jihohin da ke fuskantar hare-haren ƴan bindiga musamman a yankunan da ke makwabtaka da jihar Zamfara.

BBChausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *