fbpx
Friday, August 12
Shadow

Mata ta maka tsohon mijinta a kotun Shari’a bayan yayi wuff da aminiyarta a jihar Kaduna

Wata mata ‘yar shekara 25, Firdausi ta maka tsohon mijinta Sa’idu a kotun Shari’a dake jihar Kaduna bayan ya saketa ya auri aminiyarta.

Lauyar Fiddausi, Zainab Murtala ta bayyana cewa ya kwashe gabadaya kayan tsohuwar matar tasa ya damkawa amaruar tasa hatta kayan sawarta.

Kuma ta kara da cewa ita bai taba kama masu gida ba tunda ya aureta sai dai su riga haduwa a Otal har ya saketa sau biyu, saboda haka ya maido mata kayanta.

Amma lauyan mijin nata Abubakar Sulaiman yace karya take yiwa mijin nata, wanda hakan yasa mai shari’a Rilwanu ya daga shari’ar zuwa tara ga watan Augusta.

Leave a Reply

Your email address will not be published.