Wednesday, December 4
Shadow

“Mataimakin Gwamna A Najeriya Kamar Ba Ka Da Aiki Ne” — Tsohon Mataimakin Gwamna

Yanzu haka dai wani tsohon ministan lantarki kuma tsohon mataimakin gwamna a jihar Yobe, ya ce babban sirrin zama mataimakin gwamna da gwamnan kansa shi ne yin gaskiya da riƙon amana da kuma biyayya.

Injiniya Abubakar D. Aliyu ya ce duk da yake tsarin mulkin Najeriya ne ya tanadi muƙamin mataimakin gwamna, amma kuma bai tanadar masa wani taƙamaiman aiki ba, don haka “in dai kana so ka yi, ka zauna kawai. Abin da gwamna ya ce ka yi, ka yi. In ya ce kar ka yi, ka bari”.

A cewarsa: “Ba zancen kai Mataimakin gwamna (ne ba), ai tare muka je mu kai kamfen, ai tare muka je! Ai gwamnatin, tsarin mulki ne yake ajiye ta, to kai kuma tsarin mulki ba abin da ya ba ka”.

Karanta Wannan  A yaune Ministan kudi zai gabatar wa da shugaba Tinubu sabon daftarin mafi karancin Albashi

Tsohon Ministan ya Bayyana hakan ne a jerin hirarrakin da BBC ta yi da wasu jiga-jigan ‘yan siyasar Najeriya albarkacin cikar mulkin dimokraɗiyya shekara 25 karon farko a tarihin ƙasar.

Da aka tambaye shi, ko yana jaddada maganar nan da wasu ke ta yaɗawa a ƙasar cewa mataimakin gwamna daidai yake da matsayin safaya taya, sai Injiniya Abubakar D. Aliyu ya ƙyalƙyale da dariya, yana cewa: “Wanda ya ƙirƙiro (maganar) safaya taya ɗin nan ya yi ƙoƙari, amma ni dai ban ce haka ba”.

Ya kuma bayyana ra’ayinsa kan ci gaba ko akasin haka da yake gani an samu a tsawon shekaru 25 na mulkin jamhuriya ta huɗu, wadda ya ce a ganinsa ci gaban da aka samu bai kai na zamanin jamhuriyar ta farko ba wadda kwata-kwata ba ta fi shekara shida ba.

Karanta Wannan  Yanzu-Yanzu:EFCC ta kafa kwamiti dan binciken tsohon gwamnan jihar Kaduna malam Nasiru Ahmad El-Rufai

Daga: Abbas Yakubu Yaura

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *