Mataimakin gwamnan jihar Yobe, Idi Barde Gubana, ya rasa yaransa guda biyu sakamakon hadarin mota a kan babbar hanyar Kano zuwa Maiduguri.
Hadarin ya faru ne ranar sati wanda yayi sanadiyar mutuwar ‘dansa wanda ya radama sunan mai gidansa watao mai suna Mai Mala Buni.
Yayin da ita kuma Khadija wadda akafi sani da Siyama taji mummunan rauni aka kaita asibiti kafin ta mutu a yau ranar alhamis.
Kuma an birne ne ta a jihar bayan anyi mata janaza kamar yadda addinin musulinci ya tanadar.