fbpx
Sunday, December 4
Shadow

“Matakai guda bakwai na takaita ko kuma magance mummunan kishi ga mata”>>Sheikh Isah Ali Pantami

“Assalamau alaikum warahamatullahi wa baratauhu, wannan tunatarwane ga ‘yan uwana, musamman zuwa ga iyayenmu mata, nayi tunanin wannan tunatarwa kula ga abinda ake tunain ya faru a Abuja da kuma Zamfara, gabannin nan yasha faruwa a gurare da dama, ta inda ake tsammanin wani bangare na ma’aurata na iya cutar da wani bangare, kula da wannan, maudu’in dazan yi magana akai shine matakai bakwa, na takaitawa ko na magance mummunan kishi,musamman ga iyaye mata:
Na farko a babin adalci, mu sani cewa, kishi wani abune da Allah ta’ala ya hallici mace akai, baya taba yiyuwa a raba mace lafiyayya da kishi, saboda haka, malaman musulunci irin su ibunu Rajab, irin su imamunddabari, Rahaatullahi Alaihim, sukace ba’a mata azaba akansa, saidai in kishin yasa ta wuce gona da iri, tayi zalunci na zagin wata, ko cutar da wata, koyi mata karya, ko yimata kazafi, ko duka, ko raba wani da ransa, to anan ta wuce iyaka kuma za’a iya yimata ukuba akansa.
Baya ga wannan, a cikin hadizi da yazo cikin iriwa’ul garil, juzu’i na bakwai, shafi na tamanin, Annabi(S.A.W) ya gayamana kishi kala biyune, Akwai kishin da Allah keso akwai wanda Allah bayaso, yace kishin da Allah yakeso shine kishin da, Akwai damar ayi mummunan zato a cikinshi na aikata Haramun, misali mace ita kadaice a gurin mijinta, yayi tafiya, daya dawo, bai saba aiki da Kondom(kwaroron roba) ba, sai taga ganshi a cikin aljihunshi, ta dauka ta aje, sai shi kuma ya dawo gida a gaggauce yana caje aljihu yana so ya dauka ya boye dan kar a gani, to wannan zaisa tayi zargi a kayinsa, to wannan babu laifi, saboda yin zina Haramunne.
Amma kishin da ba’aso, shine abinda yake Halalne ga miji, mace tasa a gaba, ta damu kanta akan da abinda be daceba,(Misali) a’a wayanka tayi kara me gida, wacece ta aiko maka da sako?, a’a sakon whatsapp ya shigo, wacece ta aiko maka dashi?, a’a naga kana ta dariya, me kake karantawane, ko watace ta maka sako?, me gida baka dawo ba har yanzu, ina kakene, kodai ka tafi wajan watace?, mace ta tada hankalinta kan wadana abu bayi da kyau.
Baya ga wannan a cikin hadisin da yazo cikin Fathul bari, juzu’i na tara, shafi na dari uku da ashirin da biyar, Annabi(S.A.W) yana gayamana illar mummunan kishi, da cewa, lallai mace me mummunan kishi, wanda ba’aso, bata iya gane inane zurfin rijiya yake, ma’ana, bata ganin gabanta, da kishin ya motsa, sai ta rik hukuncin da zata rika dana sani daga baya, duk natar dake da mummunan kishi to bazata rabu da dana sani ba a cikin rayuwarta.
Matakai guda bakwai da zasu taimaka wajan magance kishi, musamman mummuna:
Akwai addu’a, a cikin addu’a akwai guda biyu, na farko akwai ” Allahumma Aaati nufusana taqwaha, wa zakkiha antakhairu man zakkaha, Anta waliyyuha wa maulaha, Addu’a ta biyu, mace ta yawaita cewa, Wahadi Qalbi, waslulsakimatasadri, watau Ya Allah ka shiryadda zuciyata, ka wankemini daudar dake cikinta.
Abu na biyu, yawan riko da kur’ani, karatunsa, sanin ma’anarsa, jin tafsirinsa, yawan kunnashi ana sauraro, yana da matukar muhimmanci, don Allah yace, da ambaton Allah zuciya ke samun abinci.
Abu na uku, yawan neman tsarin Allah ta’ala daga shedan, musali a yawaita cewa. A’uzu billahi, minashshaidanirrajim ko kuma Rabbi a’uzu bika min’ hamazatishshayadin wa a’uzu bika rabbi ayyahadrun.
Abu na hudu da zai takaita mummunan kishi, ya magance miki, (shine) yawan gaisawa da hannu, ya halatta mata su rika gaisawa da ‘yan uwansu da hannu, a cikin hadisi na muwadda imamu Malik, Allah ya masa rahama,hadisi na dubu daya da dari hudu da goma sha uku, sunnah ta karantar damu, ku yawaita gaisawa da hannu, iya tafiyar da kullin dake zuciya na gaba da kishi me muni.
Sannan kuma na biyar, shine, ku yawaita yin kyautawa junanku, zaisa kuso juna kuma zai tafiyadda mummunar kiyayya, mace ta yawaita kyauta zuwaga abokiyar zamanta, in su biyune ko uku ko hudu a wurin miji, ki yawaita siyan abu kima nusu kyauta, dan rigane, a’a dan dan kunnene, a’a kinga dan kayan marmari haka(kayan itatuwa), siyosu kiba ‘yan uwanki, yana taimakawa wajan magance wannan mummunan kishidin.
Sai na shida, shine, yawaita ambaton Alherin ‘yar uwarki, mu duba lokacin da akayiwa nana A’isha(Yardar Allah ta tabbata a gareta) kazafin tayi zina, wdda yazo cikin suratun Nur, Allah ya wanketa, Anzo an tambayi abokiyar zamanta, Zainab Bintu Jahash(Yardar Allah ta tabbata a gareta), cewa a cikin hadisin Bukhari da Musulim, shin Annabi(S.A.W) yacemata ya Zainab, me kika gani akan A’isha, me kike fahimta akan zargin da akaimata?, sai tace, Annabi na kiyaye jina da ganina, bana fadan abinda ban ganiba, bazan mata karyaba, Tace ni bansan komaiba da nana A’isha(R.A) ba sai Alkhairi, duba fa abokiyar zamane, amma tace wallahi alkahiri na sani, ta samu gurbin da za’a sake ‘yar uwarta amma sai taki goyon baya tace wannan baiwar Allah Alkhairi na sani da ita, duk da wannan ka duba Nana A’isha (R.A), Annabi ya taba tambayarta, me zakice akan Zainab?, tace wallahi ban taba ganin mata, mai addini da ta kai abokiyar zamana, Zainab Bintu Jahash ba(R.A), tare da cewa mijinsu daya amma wannan be sata yimata mummunan zato ba kuma A’isha take cewa, a duk matan Manzon Allah babu wadda take tsarana da muke gasa tare wajan samun gindin zama kamar Zainab amma kowacce maganarta akan ‘yar uwarta Aljhairine.
Sai abu na bakwai, nisantar mummunan zato da kuma bincike-bincike, Haramunne a musulunci, kamar yadda sheikh Abdullahi Binu Mudlak yake fada, yawan bide wayar miji a duba me yakeyi, a’a yawan bude Imel dinsa bada izininsaba, wannan malaman musulunci sukace be halattaba. A kasar Saudi Arabiya, dalilin duba wayar maza da mata keyi yake sabbaba kashi ashirin cikin dari na mutuwar Aure, saboda haka malamai sunce be halattaba,  Allah ya takaitawa iyayenmu mata mummunan kishi, Allah ta’ala ya taimakemu mu dasu, mu gudu tare mu tsira tare, mu shiga Aljanna tare. Wassalamau alaikum warahmatullahi wa barakatuhu.” 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Karanta wannan  YANZU-YANZU: Gobara Ta Tashi A Dakin Kwanan Dalibai A Jami'ar Dan Fodiyo Dake Sokoto

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *