fbpx
Friday, December 2
Shadow

Matan da ba sa cin nama za su iya karyewa a kwankwaso – Bincike

Matan da ba sa cin nama za su iya fuskantar yiwuwar karyewa a kwankwaso nan gaba a rayuwa, kamar yadda wani bincike ya nuna.

Masu binciken sun rika bin rayuwar mata   26,000 na tsawon shekaru 20 kuma sun gano cewa  kashi daya bisa uku na matan da ke cikin rukuni da ba sa cin nama sai  kayan lambu ko kayan itace za su iya samun karaya ko targade fiye da masu cin nama.

Kwararru daga Jami’ar Leeds sun ce wasu daga cikin matan da ba sa cin naman na iya rasa sinadaran inganta lafiyar kashi  da tsokar kashi lamarin da ke haifar da hadarin karaya.

Sai dai duk da haka mawallafan rahoton sun ce bai kamata wadanda ba sa cin nama su yi watsi da cin kayan lambu da na itace ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *