by hutudole
Akalla mata 6,800 ne a jihar Katsina za su ci gajiyar tallafin kudi na gwamnatin tarayya da nufin karfafawa da daukaka su.
Ministar kula da ayyukan jin kai, Hajiya Safiya Umar Farouk, ce ta bayyana hakan a Katsina ranar Laraba, inda ta ce sama da mata 160,000 ne za su ci gajiyar duk fadin kasar nan.

Ministar, wacce ta je jihar don kaddamar da rabon tallafin, ta ce kowane daya daga cikin wadanda za su ci gajiyar zai karbi Naira dubu 20, a matsayin wani bangare na ayyukan sanya jari na ma’aikatarta don rage tasirin COVID-19 akan matalauta da marasa karfi.
Daga nan sai Ministar ta umarci wadanda suka ci gajiyar shirin da yin amfani da damar wajen kara kudin shiga, inganta wadataccen abincin su da kuma bayar da gudummawa wajen inganta rayuwar su.
A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari, wanda Mataimakinsa, QS Mannir Yakubu ya wakilta, ya godewa gwamnatin tarayya kan dimbin ayyukan ta na zamantakewar da ta fitar da miliyoyin mutane daga talauci.