fbpx
Thursday, May 19
Shadow

Matan shugabannin jami’o’i na shirin tafiya Turkey yayin da ASUU ke tsaka da yajin aiki

Yayin da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa, ASUU ta ke tsaka da yajin aiki, su kuwa matan Shugabannin Jami’o’i na Ƙasa (Vice Chancellors) na shirin tafiya birnin Istanbul na ƙasar Turkey domin halartar wani taro na kwanaki biyar.

A cewar wata wasiƙa da Kwamitin Shugabannin Jami’o’i na Ƙasa ta fitar, za a yi taron ne daga ranar 18 ga watan Yuli zuwa 23 ga watan a Istanbul.

Jaridar Punch ta rawaito cewa wasiƙar an buga ta ne tun a ranar 5 ga watan Mayu kuma na ɗauke da sa hannun Sakataren kwamitin, Yakubu Ochefu.

Karanta wannan  Jami'an tsaro sama da 100 suna kallo aka kashe diyata amma basu yi komai ba>>Inji Baban Deborah da tawa Annabi Muhammad(SAW) batanci

A cewar Ochefu, matar ko wanne Shuagaban Jami’a ta ƙasar nan za ta biya Naira miliyan 1.5 kuɗin form din halartar taron.

Wasiƙar ta ce halartar taron wayar da kan na da muhimmanci ga matan, duba da irin rawar da su ke taka wa wajen nasarar mazajen na su a jami’o’i na ƙasar nan.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.