fbpx
Thursday, February 25
Shadow

Matar aure ta kashe budurwar Mijinta

Kotun majistare, a ranar Talata, ta ba da umarnin tsare wata matar gida ’yar shekara 18, Suwaiba Shuaibu, kan zargin daba wa wata mata da mijinta ke neman aure mai shekara 17 wuka.

Mai gabatar da kara, Asma’u Ado, ta fadawa kotun cewa a ranar 1 ga watan Janairun 2021, da misalin karfe 10 na dare, wanda ake kara ta kira matar da mijinta zai aura, Aisha Kabir, a waya.
Asma’u ta bayyana cewa, “Ana cikin haka ne, wanda ake karar ta yaudari yarinyar kuma ta yaudare ta zuwa wani gida da ba a kammala ba a kauyen Gimawa, sai ta far matar, ta daba mata da wuka mai kaifi a wuyanta da kirjinta.
“A ranar 2 ga watan Janairun, mahaifinta, Kabiru Jafaru ya same yarinyar a gidan da ba a kammala ba, kuma aka garzaya da ita babban asibitin Tudun Wada inda aka tabbatar da cewa ta mutu,” ta kara da cewa laifin ya ci karo da sashi na 221 na Penal Code.
Wadda ake tuhumar ta musanta aikata laifin.
Babban alkalin kotun, Mustapha Sa’ad-Datti, ya ba da umarnin a ci gaba da tsare wadda ake kara a gidan gyara har sai an samu shawara daga ofishin Daraktan Lauyan Jama’a (DPP), sannan ya dage shari’ar zuwa ranar 17 ga Maris, 2021.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *