fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

‘Matar data kashe ‘ya’yanta a Kano tana da Aljanu’

Mahaifiyar matar da ake zargi ta kashe ƴaƴanta guda biyu a jihar Kano da ke Najeriya ta ce ‘yarta ta daɗe tana rashin lafiyar da ke da nasaba da iskokai.

 

A ranar Asabar ne rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta tabbatar da mutuwar wasu yara biyu mace da namiji yan shekara uku da kuma shida da ake zargin mahaifiyarsu ce ta kashe su.

 

Lamarin wanda ya faru a Unguwar Sagagi Layin ‘Yan Rariya a birnin Kano, da farko an bayyana cewa sabani ne da mijinta saboda ya yi mata kishiya a watannin baya ya kai ga kisan ƴaƴansu.

 

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce jami’anta sun kama matar yanzu haka tana hannunsu, kuma ta tabbatar da cewa ita ta kashe ƴaƴanta, kamar yadda kakakin rundunar ya shaida wa BBC.

 

Ya kuma ce bayan matar ta kashe yayanta biyu ta kuma raunata wata yarinya yar shekara 10.

 

Amma kakar yaran da aka kashe Binta Ado Nababa ta shaida wa BBC cewa ƴarta ta shafe tsawon wata uku ba ta iya bacci, “tana cewa kullum da dare ana zuwa ana danne ta ana shake ta. Ta fi wata uku ba ta bacci, da dare ana yi mata gurnani irin na dodanni.

 

“Da farko ban ɗauki maganarta da muhimmanci ba amma na faɗa mata cewa ta dinga yin addu’a kuma ta faɗa wa mijinta,” in ji mahaifiyar matar.

 

Sai dai mahaifiyar ta ce tun da ta aurar da ƴarta shekara shida da suka gabata, ƴarta take tafka rikici da mijinta. “Kullum faɗa suke da mijinta,” in ji ta.

 

Mahaifiyar ta ce ta taɓa zuwa neman kashe auren ƴarta saboda rikicin da kullum suke yi da mijinta.

 

“Saboda ita ta huta da rikicinta da mijinta. Wata ɗaya da zuwa gidansa suke tafka rigima, kuma irin rikicin da suke yi ne har dangin mijin suke tunanin akwai abin da ke damunta,” in ji ta.

 

Mahaifiyar ta kuma daga baya ƴarta ta samu rashin lafiyar, kuma ƴarta ta taɓa zuwa wurin malami har aka yi mata karatu amma rashin lafiyar ta ƙara tsanani.

 

Abin da mahaifiyar matar ta ce kan kisan jikokinta

Sai ta rantse ta ce “wallahi tallahi ba ita ta kashe su ba kuma ba ta san wanda ya aikata kisan ba.”

 

Da ta zo nan gidan ta ce ba za ta iya kwana da kowa a gida. Ta ce tsoro take yi tana son a ba ta babba da za ta iya zama da shi.

 

Lokacin da ta shigo na tambaye ta, ko lafiya ta zo, ta ce lafiya lau ba komai. Amma zazzabi take ji ba ta da lafiya.

 

Da mijin ya zo sai ya ce matarsa ta yi masa waya cewa, ya zo ga yayanta nan za su kashe ta.

 

Uwar ta ce ba ta san yanzu inda ƴarta ta ke ba tun lokacin da mijinta ya tafi da ita.

 

Abin da ƴan sandan Kano suka ce

Kwamishinan 'yan sandan jihar Kano

Kakakin ƴan sandan Kano Abdullahi Haruna ya ce ba yanka ƴaƴanta ta yi ba, sassara su ta yi da adda da taɓarya.

 

Ya ce bayanan da suka samu suka taimaka har suka kama matar misalin karfe 10:30 na dare bayan ta gudu.

 

Ta shaida wa ƴan sanda cewa yaran ne suka ɗauki wuka suna neman halaka ta, daga nan kuma ta shiga dukansu da taɓarya da kuma sassare su da adda.

 

Ya ce kwamishinan ƴan sandan jihar Kano ya bayar da umurni a dawo da ita babban sashen binciken kisan kai domin faɗaɗa bincike. Kuma za su ci gaba da bincike kan abin da ya sa ta aikata kisan.

 

Haka kuma ƴan sandan za su yi bincike kan mijin domin gano ko yana da hannu a aikata kisan.

 

Lamarin ya daure wa mutane da dama kai a unguwar ta Sagagi da ma fadin jihar Kano, musamman makwabtan gidan da lamarin ya faru, inda suke cewa a iya sanin da suka yi wa matar ba ta da tabin hankali haka kuma ba a san ta da shaye-shaye ba.

BBChausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.