Matar da ake zargin jami’in dan sanda dake ofishin Adeeke, CSP Ige Adekunle ya lallasata a Iwo dake jihar Osun, Blessing Mba ta bata
Inda rahotanni suka bayyana cewa matar ta bar gidanta ne dake kallon ofishin ‘yan sandan da yaranta guda biyu ranar lahadi.
Amma mai magana da yawun hukumar ta jihar SP Yemisi Opalola ta bayyana cewa Blessing ta tserewa hukuma bayan da suka ce ranar lahadi zasu kaita Osogbo taga kwamishinan su hedikwata.
A ranar 31 ga watan mayu ne ake zargin shugaban ‘yan sandan ofishin na Adeeke yasa yaransa suka lallasata.