Wannan shima wani zane ne da akayi akan maganar kisan da Maryam ta yiwa mijinta Bilya da wuka saboda kishi, labarin ya saka mutane sun fara canja tunani akan irin matan da zasu aura ga wadanda basu yi aureba ga wadanda kuma suke da aure sun fara dain zasu yi hattara da wayoyinsu, idan kuma kasan matarka me binciken wayace to saika dena boye mata komai dan kar zargi ya shiga.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Wannan maganar ta sama itama tana daya daga cikin wadanda aka tika yawo dasu a kafafen watsa labarai da muhawara na yanar gizo da aka rika barkwanci dasu maganartana cewa “Duk wanda yasan matarshi na dubawayarshi to yayi magana a taimakeshi da maganin tauri”
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Haka shima wannan bayanin dake kasa, an daukoshine daga dandalin wani da ake kira da Mudassir, inda yayi fadakarwa akan wannan batu cikin raha:
TAMBAYA : Umma Ina babana?
AMSA: ya mutu?
TAMBAYA: me ya same shi ?
AMSA: kashe shi aka yi..
TAMBAYA: wa ya kashe shi?
TAMBAYA: shin za ki ce ni ce?
shin idan ma kin tsalleke hukuncin kisa kin gama zaman gidan dankande kin fito, za ki iya yawo cikin yan’uwanki mata?
Shin idan wani ya kyalla ido ya ce yana sonki ya yi miki tambaya shigen wadda diyarki ta yi miki wace amsa zaki ba shi?
KASH!!! Amsar ita ce zunzurutun NADAMAAA!!!! Allah ya nisanta mu da masu Hali irin Naki…..
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});