Tsohuwar tauraruwar fina-finan Hausa, Mansurah Isah, Matar Sani Musa Danja ta bayyana ra’ayinta akan batun Bilya da ake zargin matarshi da daba mishi wuka wanda hakan yayi sanadin rasuwarshi.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Mansurah a cikin wani zungyreren rubutu da tayi tace mutane nata tambayarta akan tayi sharhi akan wannan lamari, amma babu abinda zatace sai Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un. Ta fara da cewa abinda ya faru da Maryam zai iya faruwa da kowa, domin jarabawar Allah na bullowa ta hanyoyi daban-daban, zata iya zuwa ta yanda ba’a tsammani, ta kara da cewa kawai abinda mutum zai rike shine addu’a domin idan dai kana raye komai zai iya faruwa dakai.
Ta kara da cewa akawai ma’aurata da ake samun suna fada suyiwa juna munanan kalamai da fata, harma suyi amfani da makamai masu hadari wajan fada da juna amma sai Allah ya karesu irin abinda ya faru da maryam be faru da suba.
Ta kara da cewa ita matar aurece kuma tasan cewa aure ba abune me sauki ba, duk irin son da kukewa juna dolene sai anyi samu irin wannan rashin jituwar na lokaci zuwa lokaci, kawar da kai da hakuri da gani ka nuna kamar baka gani ba shine zai kawo zama n lafiya.
Ta ce tasan abinda Maryam ta aikata sharrin shedanne kuma ya kamata a hukuntata, tasan cewa ita kanta a yanzu tana dana sanin abinda ta aikata, iyayentama suna cikin kunci, musamman mahaifiyarta, tasan cewa tasha zagi da Allah wadai a bakin Duniya. Amma ma’aurata su rika gayawa juna gaskiya, kada ka gayawa mace cewa wai ita kadaice daga ita bazaka karo aure ba kema kin san hakan karyane..
Ta kara da cewa iyaye zasu baiwa dansu tarbiyya amma abokai da yanar gizo sai ta batawa yaro tarbiyya cikin kankaninlokaci.
A karshe mansurah tace tasan cewa indai Maryam tayi nadama ta tuba to tabbas tana da tabbacin cewa Allah zai yafemata.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});