fbpx
Saturday, June 10
Shadow

Matar data kashe mijinta:An gurfanar da Maryam Sanda, Mahaifiyarta da ‘yan uwanta a Kotu

An gurfanar da matan da ake zargi da kashe mijinta, Maryam Sanda da mahaifiyarta da kuma ‘yan uwanta a gaban kotu. A wannan karon, an gyara tuhumar da ake yi mata inda aka tuhume ta da kashe mijinta, Bilyaminu Bello Halliru, ta hanyar daba masa wuka da sauran makamai masu hatsari.

Sai dai Maryam ta musanta tuhumar.
Har ila yau an tuhumi mahafiyarta, Maimuna Aliyu da ‘yan uwanta Aliyu Sanda da Sadiya Aminu da laifin goge hujjar kisan kai domin kubutar da Maryam Sanda daga fuskantar da shari’a kan laifin kisan kai.
‘Yan uwan Maryam din dai sun musanta tuhumar da aka yi masu.
Da aka fara gurfanar da Maryam dai, lauyan rundunar ‘yan sandan birnin tarayyar Najeriya, Abuja, James Idachaba, ya nemi kotun ta ba shi lokacin domin ya gyara tuhumar da ake yi wa wadda ake zargin bisa sabbin bayanai da rundunar ‘yan sandan birnin ta samu.
Yayin zaman kotun na ranar 7 ga watan Disamba domin jin sabuwar tuhumar, sai lauya James ya ce bai samu ya bai wa sauran wadanda ake tuhuma da aikata laifi kan lamarin sammaci ba.
Saboda haka sai kotun ta ba shi mako daya domin ya gabatar da sauran wadanda ake zargi da aikata laifi a lamarin.

bbchausa.

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *