fbpx
Saturday, May 28
Shadow

Matar data kashe mijinta:”Maryam bata barin mijinta sakat, idan ya fita gida duk bayan minti talatin sai ta kirashi”>>Abokin Bilya

Wasu abokan marigayi Bilya Bello da ake zargin matarshi da kasheshi sun shirya wani dan karamin taro na tunawa dashi inda suka mai addu’o’in samun Rahama da jin kan Allah, wasu daga cikin abokan nashi da ‘yan uwa sun zanta da manema labarai iinda suka bayyana irin rashin da sukayi da kuma fatan da suke dashi akan wannan lamari.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Wani dan uwanshi ya bayyana cewa Bilya baya cin amanar matarshi kamar yanda ake watsa wasu labarai na karya a shafukan sada zumunta da muhawara na yanar gizo, ya kuma kara da cewa yayi rashin dan uwa kuma aboki amma shi abinda ke bashi amamaki akan wannan kisa da matarshi tayi mishi shine, kwata-kwata bata nuna alamar nadamaba, kamar ba ita ta kasheshi ba ko kuma kamar ma ba mijinta bane ya mutu, ya kara da cewa ‘yan uwanta, harda mahaifiyarta sun zo sun musu gaisuwa.
Saidai jiya a gurun sauraron shari’ar Maryam a kotu taje rike da jaririyarta da kur’ani tana karantawa da kuma carbi a hannunta tana ja, a lokacin shari’ar Maryam har fashewa tayi da kuka a bainar jama’a.
Wani abokin Bilya da shima aka zanta dashi akan rasuwar shi ya bayyana cewa abokinshi yayi hakiri da matarshi dan gaskiya tana matukar takura mishi , daya fito waje, irin da yammar nan suyi hira irin ta bokai ko kuma su zagaya gari, ba’a yin mintuna talatin zuwa awan daya sai matarshi ta kirashi, ya koma gida, kai a karshe ma dole saidai idan suna son ganin abokinnasu su bishi gida dan suyi hira, ya kara da cewa idan suna tare a waje, da an dan jima har tsokanarshi suke su cemai to yanzu zata kira ko kuma bata kira bane?. Ya kara da cewa wannan abinda ta aikata irin abinnanne na a fasa kowa ya rasa, idan ita zata rasashi to babu wadda zata sameshi
Sun dai bayyana cewa ba daidai bane ace wai dan mutum yayi kisa da gangan kawai dan yana da diya sai a tausaya mishi, kamata yayi ma ace a rabata da diyarnan, domin ba’asan meke cikin zuciyartaba yanzu haka. Haka kuma idan an sameta da laifi kamata yayi a mata hukunci irin na wanda ya kashe mutum.
Wata itama dake gurin ta bayyana ma’auratan a matsayin masu son junansu amma taki tayi wani sharhi akan lamarin, tace watakila akwai wani abu dake damun Maryam a zuciya shiyasa ta aikata abinda ta aikata.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Karanta wannan  Hotunan wadanda ke neman takarar gwamna a jihar Kano
Oaktvonline.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.