(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Dikko mustafa ya bayyana cewa abokinshi, marigayi Bilya mutumin kirkine, saidai kash, beyi dacen mataba. Yaci gaba da bayar da labari inda yace lokacin da zai auri maryam ta kuma yi kokarin rabashi da matarshi, a nanne suka saba, domin Shi Dikko yace bai goyi bayan Bilya ya saki matarshi ya auri maryam ba amma a wancan lokacin soyayya ta rufewa Bilya ido, baya ganin abinda suke hango mishi.
Dikko yace abinda yake sosamai rai shine idan ya tuna yanda suka kyale Bilya da Maryam, watakila da basu kyaleshiba da haka bata faruba, da sun bashi shawara akan yanda zai magance matsalar gidanshi. Yace amma yanzu lokaci ya kure, saidai suyi mai fatan Alheri.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});