fbpx
Sunday, August 7
Shadow

Matar Tinubu ba karamar kirista bace fastuwace saboda haka APC ba don muzgunawa Kirista ta tsayar da Musulmai a matsayin ‘yan takararta na shugaban kasa ba, cewar Kashim Shettima

Abokin takarar Tinubu wanda ake ta cece kuce akansa, Kashim Shettima shima ya tofa albarkacin bakinsa kan tsayar da Musulmai da APC tayi.

Inda yace uban gidan nasa wato Tinubu bai zabe shi domin su muzgunawa mabiya addinin Kirista ba saboda matar Asuwaju babbar Kirista ce kuma fastuwa.

Sannan ya kara da cewa dan takarar shugaban kasar na jam’iyyar APC hatta yaran shi bai takura masu akan sai sun zama Musulmai ba.

Sabon haka salon siyasar ne yazo da hakan amma da wata manufa suka yi hakan ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.