Matar farko ta tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump, Ivana ta mutu tana ‘yar shekara 73.
Donald Trump ya bayyana hakan ne a kafar sada zumunta kamar iyalanta suma suka bayyana.
Inda yace ta mutu ne a New York a gidanta na Manhattan ranar alhamis. Trump nada yara uku da Ivana, Donald Jr, Ivanka da kuma Eric.
Sannan ya kara a cewa suna matukar alfahari da ita kamar yadda take alfahari dasu, kuma suna fatan zata huta lafiya.