‘Yan kasuwa da Matasa da aka rusawa shaguna a jihar Naija sun hada kai inda suka kaiwa gidan mataimakin Gwamnan, Ahmad Getso hari.
Daya daga cikin ‘yan kasuwar, Malam Murtala Ahmad ya bayyana cewa ba’a sanar dasu ba kawai saidai gani suka yi ana rushe musu shaguna.
Yace kawai jami’an gwamnati sun ce ta fita daga shagonne ba tare da barinshi ya dauki komai ba inda suka fara rushewa.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya,NAN ya tuntubi kakakin mataimakin gwamnan, Hajiya Maimuna Kolo inda ta bayyana cewa shi mataimakin gwamnan ba ruwansa.
Shima shugaban hukumar kula da tsare-tsaren birane na jihar, Mr. Moses Dunia yace zasu ci gaba da wannan aiki.
“I was just sitting in my shop and they said come out; their bulldozer was already stationed in front of my shop and immediately they removed me forcefully, their bulldozer brought down my entire shop without allowing me to pick my cash, goods and other valuables.