fbpx
Saturday, September 19
Shadow

Matasa sunyi zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da kisan gilla a Kudancin Kaduna

Wasu matasa sun taru a ranar Asabar don nuna rashin amincewarsu da abin da suka kira “kashe-kashen da ba dalili a kudancin jihar Kaduna”.
Sun bayyana lamarin cewa “abin takaici ne” la’akari da kasancewar jami’an tsaro a yankin.
Mista Nasiru Jagaba, Shugaban Matasa na kasa, kungiyar Middle Belt, wanda ya jagoranci zanga-zangar ta hanyar Yankin NNPC, Titin Kachia, Kaduna, ya yi zargin cewa makirci ne a cikin kashe-kashen da ke faruwa.
Jagaba, tsohon shugaban kungiyar Matasan kungiyar Jama’ar Kudancin Kaduna, ya fada wa Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN) cewa ana kashe mutanen duk da da kasancewar jami’an tsaro da aka tura domin tabbatar da zaman lafiya a yankin.
Ya ce: “Mun zo ne yau don wayar da kan jama’a game da kashe-kashen da ke faruwa a Kudancin jihar Kaduna.
“Muna son jama’a da ma na cikin gida su san yadda ake kai hare-hare kan al’ummomin Kudancin Kaduna duk da dokar ta-baci da gwamnatin jihar ta sanya a yankin.
“An samu jerin hare-hare a cikin ‘yan lokutan nan da adadin mutane dayawa wadanda suka rasa rayukansu, amma har zuwa yanzu ba a kama kowa ba.
“Wadanda abin ya shafa ne kawai ake kama a maimakon maharan, wadanda ke  shiga yankin… kuma suna aiwatar da ayyukan ta’addancinsu ba tare da wani kalubale ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *