
Daga Comr Nura Siniya
Tsohon Sanata mai wakiltar shiyyar Daura a jihar Katsina Sen. Ahmad Babba Kaita, ya bayyana cewa matashin Najeriya ba Taliya ko ‘yan kudi yake bukata daga wajen ‘yan siyasa face a gina rayuwarsa don gobensa ta yi kyau.
A cewar sa, Sanata Kaita rayuwar matasa a Najeriya ba za ta inganta da taliya ko kyautar naira daga hannun ‘yan siyasa ba. Ya kuma ce abubuwan da matasa ke buƙata da gaske sune: tsaro mai kyau, ingantaccen ilimi da kuma samun aikin yi ko sana’ar dogaro da kai.
Sanatan ya jaddada cewa waɗannan ginshiƙai su ne tushen da ya gina siyasarsa a kai, kuma yana fatan ci gaba da bin wannan hanya don ganin rayuwar matasa
A ƙarshe ya ce Ina siyasa ne don a gina rayuwar matasa. Ba wai domin jama’a su sa ni a dama da su ba. Ina fatan ganin matasan Najeriya sun fita daga kangin rashin tsaro, jahilci da rashin aikin yi,” in ji shi.
Wane fatan alheri za ku yi masa?