fbpx
Tuesday, May 17
Shadow

Matashi dan Najeriya ya kashe kansa bayan ya tambayi mahaifinsa Dubu 50 amma mahaifin yaki bashi

Matashin dake aji na 2 a jami’ar Joseph Sarwuan Tarkaa dake jihar Benue ya kashe kansa.

 

Ogbonna Shedrach, ya kashe kansa ne bayan da ya tambayi mahaifinsa Naura N50,000 amma mahaifin nasa yaki bashi kudin.

 

Kakakin jami’ar, Comrade Zaki Christian, ne ya bayyana haka inda yace matashin me shekaru 20 ya kashe kansa saboda matsalar da ya samu da ‘yan gidansu.

 

Yace kamin mutuwar matashin, yayi sa in sa da mahaifinsa kan kin bashi dubu 50 ya warware wasu matsalolinsa.

Karanta wannan  Gwamnatin Najeriya ta ja kunnen kamfanin Facebook

 

Yace matashin ya kashe kansa ne ta hanyar rataya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.