fbpx
Sunday, February 28
Shadow

Matashi ya kashe kansa ta hanyar yanke Mazakutar sa a Kano

Rundunar ƴan sandan jahar Kanon Najeriya ta tabbatar da mutuwar wani matashi Mustapha Muhammad mazaunin unguwar kurna layin Mallam Na Andi da ake zargin ya kashe kansa da kwalba.

Rudunar ƴan sanda tace matashin ya kashe kansa ne bayan ya kulle kansa a wani gida dake unguwar Masukwani a birnin Kano, ta hanyar cakawa kansa gilashin tagar ɗakin da ya shiga a gidan da ya kulle kansa.

Alamarin ya faru ne a ranar Lahadi, bayan samun rahoto da ƴan sandan suka yi.

An kuma same shi ya yanka al’aurarsa.

Wasu yan uwansa sun ce yana da fama da rashin lafiyar taɓin hankali.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *