Matashi Ya Sha Fiya-fiya Ya Mutu Saboda Ƙin Taimakon Sa Kan Ciwon Ƙafa Dake Damunsa
Daga Imam Aliyu Indabawa
Wani mutum da ba a san ko waye ba ya kashe kansa ta hanyar shan fiya-fiya, kafin rasuwarsa ya rubuta wasiyya yana mai roko cewa bayan mutuwarsa a yi masa sutura da jana’iza kamar yadda musulmi ya koyar.
A wasiyyar tasa kamar yadda Arewa Radio suka rawaito, ya bayyana cewa ya jima lokaci mai tsayi yana neman taimakon aikin ƙafar da ke damun sa, amma bai sami ba. Wanda ƙuncin rayuwa da zafin ciwo ya kai shi ga shan fiya-fiya ya mutu.
Sai dai bai faɗi sunan garin da ya fito ba. Wannan ƙalubale ne ga al’ummarmu masu hali su sani cewa su ababen tambaya ne gobe ƙiyama kan dukiyarsu.
Allah ya yi mana karshe mai kyau.