Matashi Ya Yi Garkuwa Da Kansa, Inda Ya Karbi Milyan Daya
Wani dan asalin jihar Adamawa, mai suna Israel Emmanuel ya yi garkuwa da kansa, ya karbi naira milyan daya a matsayin kudin fansa.
Israel dan shekara 19, ya hada kai da wasu abokansa biyu Zakka Nuhu da Fartaci Mustapha, suka taimaka masa ya yi garkuwa da kansa, ya boye a wani guri, suka kira mahaifinsa, suka karbi naira milyan daya a matsayin kudin fansa, sannan ya koma gida.