fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

‘Matata Kullum Sai ta Lakadamin Duka, Wani Magidanci Ya bukaci Kotu ta raba Auransu da Matarsa

Wani magidanci ya ruga gaban kotu dake da zamanta a Mapo a jihar Ibadan a ranar Juma’a ina ya bukaci kotu da ta datse igiyar auransa da matarsa mai suna Bolaji kasancewar tana lakada masa doka tare da yi masa barazana, kamar yadda ya shaidawa kotun.

Sai dai Matar ta musanta zargin, inda ta shaidawa kotu cewa, Mijin nata baya kula da ita yadda ya kamata, hasalima ko kwana a gida bayayi.

Da yake yanke hukunci, Shugaban kotun, Cif Ademola Odunade ya raba auran nasu wanda Ma’auratan sun shafe watanni 18 a matsayin miji da mata.

Karanta wannan  Na gaji da daukar nauyin kaina aure nake nayi, cewar tauraruwar Nollywood

Sai dai bayan yanke hukuncin Al’kalin kotun ya mika Dan da suka haifa zuwa ga matar, inda kuma kotu ta bukaci mijin ya ringa biyan naira 5,000 a matsayin kudin kula da yaron a kowanne wata.

 

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.