Wani ma’aikacin gwamnati, Oyeniyi Oyedepo, a ranar Juma’a, ya fadawa wata Kotun Al’adu da ke Mapo a Ibadan da ta kawo karshen aurensa da Iyabo, na shekara 14, saboda matarsa tana marinsa a duk lokacin da ya ladabtar da ’ya’yansu hudu.
NAN ta ruwaito cewa Oyedepo a karar da ya shigar ya fadawa kotu cewa matar sa ta lalata auren su.
“Duk lokacin da na buge wani daga cikin yaranmu saboda rashin da’a, Iyabo na kan bacin rai kuma za ta mare ni.
“Tana da rashin biyayya da rashin ladabi,” in ji Oyedepo.
A martaninta, Iyabo ta yarda da sakin inda ta kara da cewa mijinta mai neman mata ne.
Ta fadawa kotu cewa mijinta ya cika fada kuma mai kazanta ne.
“Ee, na mare shi. Amma saboda ya doke ni ne ya ce in bar gidansa.
“Bugu da ƙari, ina son wannan auren ya mutu saboda ba na ƙaunatarsa kuma,” in ji ta.
Da yake yanke hukunci, Shugaban Kotun, Cif Ademola Odunade, ya gaya wa ma’auratan cewa auren nasu na iya ci gaba idan har za su iya hakuri.
Ya kuma dage karar har sai ranar 6 ga Afrilu, domin ci gaba da sauraren karar.