fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Matata ta yaudareni na sayi mashin a hannun Saurayinta>>Miji ya gayawa kotu

Wani magidanci, Isaac Ayodele a Ibadan ya gayawa kotun dake Mapo cewa matarsa, Omotayo ta yaudareshi ta kaishi wajan saurayinta ya sayi Mashin akan Haya Faces.

 

Yace matarsa na zuwa wajan aiki amma da ya samu aiki sai yace ta daina fita. Yace daga baya ya rasa aikin nashi inda yace ta rika yin abincin sayarwa.

Annan me yace ta fara bin maza inda ta hadashi da daya daga cikin mazan da take bi ya sayi babur a hannunshi.

 

Saidai a nata bangaren tace Mijin nata da ta tambayeshi kudi sai duka. Kuma lokacin da ya rasa aikinshi an koresu daga gidan hayar da suke, dan uwanta ne ya kama musu gida. Sannan ta masa hanya ya samu mashin amma ya ki biyan kudin mashin din.

 

Maishari’a, Ademola Odunade ya hukaci da su je su kawo karin hujjoji qkan zarge-zargen nasu saidai ya basu shawarar cewa su yi sulhu tsakaninsy ya fi Alheri.

 

Ya kuma daga sauraren karar zuwa 13 ga watan October.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.