fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Matata Tana Azabtar Dani- Wani Magidanci Da Yake Neman Agaji

Daga Tonga Abdul Tonga

Wani Magidanci Dan Shekaru 33 da haihuwa ya koka matuka saboda yadda matarsa daya ke tare da ita take mugun azabtar da ciki har da masa dukan tsiya.

Yace ya aureta shekaru 5 da suka wuce. Komai yana tafiya daidai sai shekaru 2 da suka gabata zuwa yanzu ta sauya sosai fiye da a baya can.”

“Matata na auro a gidan masu kudi. Iyayen ta masu abun duniya ne, don haka komai na gidan kawo mana akeyi daga gidansu. Baya ga dan aikin da ake biya na, kudin kashewa ma Babanta ke bani duk wata. Wannan yasa sai abunda take so akeyi a gidan. Hatta Jima’i sai randa take so muke yi”.

Karanta wannan  'Yan ta'addan ISWAP sun dauke manoma shida a jihar Borno

Inji mijin dake neman doki.
Yace duk wani aikin gidan hatta kula da yar da suka haifa shi yake yi da zaran ya dawo daga aiki. Haka tsaftace gida har da wanke motocinta duk taki yarda a kawo masu aiki yace duk shi zai yi.”

Sai dai daga karshen jawabin nasa yace kwadayin abun hannunta ne ya jawo masa tun a farko. Gashi yanzu tana azabtar da shi kuma yana matukar sonta.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.