Shugaban rukunin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya tabbatar da cewa matatar man Dangote za ta fara aiki kafin karshen gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari a shekarar 2023.
Ya bayar da wannan tabbacin ne a ranar Juma’a yayin da yake gabatar da tambayoyi daga manema labarai na fadar shugaban kasa bayan ganawarsa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Dangote, wanda aka tambaye shi game da lokacin da matatar man za ta fara aiki, ya ce da yardar Allah, shugaban kasa zai zo ya kaddamar da aikin kafin karshen wa’adin mulkinsa.