Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, Matsalar kungiyar malaman jami’a ta ASUU ba karama bace.
Ministan yada labarai, Alhaji Lai Muhammad ne ya bayyana haka ga manema labarai bayan zaman majalisar zartaswa da shugaba Buhari ya jagoranta.
Yace amma duk da matsakar ba karama bace, suna iya iyawarsu wajan ganin an maganceta.