Mai Alfarma Sarkin Musulmi a Najeriya Muhammad Sa’ad Abubakar III ya buƙaci al’ummar Musulmi su fara gudanar da addu’o’i na alƙunutu game da kashe-kashen da yankin arewacin ƙasar ke fama da shi na ‘yan bindiga.
Kazalika sarkin ya nemi dukkan masallatai da majalisun tattaunawa a faɗin Najeriya da su dage da addu’o’i “a irin wannan lokaci na bala’o’i don neman tausayin Allah”.
Wata sanarwa daga ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) wadda sarkin Musulmi ke jagoranta ta ce an yi kiran ne saboda ya zama dole.
“Wannan kiran ya zama dole idan aka duba yadda ake ci gaba da kashe rayuka da wulaƙanta su gabagaɗi kamar yadda muka gani a Sokoto da Gidan Bawa da Beni-sheikh da Kaga (Jihar Borno),” a cewar sanarwar da sakataren JNI Dr. Khalid Abubakar Aliyu ya sanya wa hannu.
Tun daga farkon makon da ya gabata; ‘yan fashin daji sun ƙona mutum 23 da ransu a cikin motar fasinja a Jihar Sokoto sannan suka sake kashe uku tare da sace wasu da dama; ‘yan bindiga sun kashe mutum aƙalla 15 a masallaci a Jihar Neja; an kashe kwamashina a Jihar Katsina a cikin gidansa.