Gwamnan jihar Ogun Dapo Abiodun ya bayyana cewa al’ummarsa dake boda suna rayuwa cikin fargaba saboda maharan dake kawo masu hari.
Ya bayyana hakan ne bayan sabon shugaban hukumar dake lura da shige da fice ta jihar, Yakubu Jibrin ya kai masa ziyara a gidansa dake Abeokuta.
Inda yace masa maharan suna ketare boda ne su shigo Najeriya musamman daga kasar Benin Republic su aikata ta’addancin nasu kuma su koma.
Saboda haka yana shawartar shi daya hada kai da sauran hukumomin tsaro kamar soji da ‘yan sanda da kuma DSS domin su shawo kan matsalar.