Shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Adamu ya bayyana cewa babau shakka jam’iyyar ce zata lashe zabe a shekarar 2023.
Tsohon gwamnan jihar Nasarawa ya bayyana hakan ne yayin dayake ganawa da manema labarai na Arise TV.
Adamu ya aminta cewa Najeriya na fama da matsalar tsaro, amma yace ba akansu aka fara samun matsalar tsaro na saboda haka InshaAllahu zasu lashe zabe.
A karshw yace suna nan suna cigaba da shirye shirye kuma dama sune ke mulki a jihohi 22 cikin 36 na kasa Najeriya.