Gwamnan jihar Imo Uzodimma ya bayyanawa ‘yan jiharsa cewa kar su damu su ba sai sun sayi bindugu don kare kanwunan su ba.
Ya bayyana masu hakan ne bayan ya gana da shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari a babban birnin tarayya Abuja.
Gwamnan ya fadi hakan ne biyo bayan abokinsa Gwamna Matawalle ya cewa ‘yan jiharsa ta Zamfara su sayi bindugu don kare kansu.
Inda yace shi ‘yan jiharsa ta Imo ba sai sun saya bindugun ba domin jami’an tsaro na iya bakin kokarinsu wurin kare rayukan al’ummar jihar.