fbpx
Monday, August 15
Shadow

Matsalar tsaro: Gwamnan jihar Kogi ya dakatar da sarki tare da shugaban karamar hukuma a jihar

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya dakatar da sarkin gargajiya na Eganyi dake karamar hukumar Ajaokuta, Alhaji Musa Isa Achuja biyo bayan saba dokar daya yi wanda hakan yasa ‘yan sanda uku da ‘yan vigilanti bakwai suka rasa rayukansu.

Yayin da shima shugaban karamar hukumar ta Ajaokuta Hon. Mustapha Aka’aba gwamnan ya dakatar dashi kuma bashi nan da awanni 24 ya daya amsa wannan dakatarwar daya yi masa.

Sakataren gwamnan ne ya bayyana hakan a yau ranar lahadi wato Mohammed Onogwu, inda kuma ya gargadi sauran sarakunan jihar cewa duk wanda ya aikata irin wannan laifin shima zai fuskanci hukunci.

Leave a Reply

Your email address will not be published.