fbpx
Monday, August 15
Shadow

Matsalar Tsaro; Ku sha kuruminku na ba jami’ai damar gamawa da ‘yan bindigar kasar nan, cewar shugaba Buhari

Shugban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari yayi Allah wadai kan hare haren da ‘yan bindiga ke kaiwa jihar Kaduna, Sokoto da kuma Filato.

Inda shugaban yace yana mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan mutanen da suka rasa ‘yan uwansu sannan kuma yan yiwa masu jinya fatan samun lafiya akan lokaci.

A karshe yace gwamnatinsa ba zata taba yin kasa a gwowa ba face ta fatattaki ‘yan bindigar dake kaiwa al’ummarta hari, kuma yaba hukuma damar gama dasu bakidaya.

Hadimin shugaban kasar Garba Shehu ne ya bayyana hakan a yau ranar talata.

Leave a Reply

Your email address will not be published.