Wasu tsagera da ake kyautata zaton cewa ‘yan bindiga ne sun kaiwa AIG hari wato mataimakin shuganan ‘yan sandan Najeriya dake lura da zone 12.
Sun kai masa harin ne a jiya ranar talata biyu ga watan Augusta a jihar Bauchi tare da tawagarsa.
Kuma sun jigata mataimakin shugaban hukumar da alburusai yayin da kuma suka kashe wasu daga cikin dakarun nasa.