fbpx
Monday, August 15
Shadow

Matsalar Tsaro: ‘Yan bindiga sunyi garkuwa da shugaban likitoci a jihar Zamfara

Kungiyar likitocin Najeriya ta NMA a jihar Zamfara ta tabbatar da cewa ‘yan bindiga sunyi garkiwa da membanta, likita Mansur Muhammad.

Shugaban kungiyar NMA din ta jihar, likita Mannir Bature ne ya tabbatar da wannan labarin inda yace Mansur likita ne dake aiki a babban asibitin jihar.

Inda yace wannan lamarin ya faru ne ranar asabar a Mashayar Zaki kan hanyar Dansadau-Magami a jihar Zamfara.

Kuma yayi kira al’ummar jihar su taya su da addu’a yayin da suma zasu cigaba da iya bakin kokarinsu don ganin cewa ya dawo gida lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.