A makon daya gabata ‘yan bindiga suka kaiwa rundunar sojoji hari akan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja ta wurin tsaunin Zuma.
Wanda tarahotanni suka bayyana cewa sun kashe wasu daga cikin sojojin kuma sun jiwa wasu rauni a harin kwantan baunar da suka kai masu.
Kuma yanzu ‘yan ta’addan ISWAP sun bayyana cewa sune suka kai wannan harin, a yau ranar lahadi ne ‘yan ta’addan suka bayyana hakan.
Kuma a baya dama sun bayyana cewa sune suka kai hari gidan Kurkuku na Kuje dake babban birnin tarayya.