Hukumar gudanar da zabe, INEC ta tabbatar da cewa za’a gudanar da zaben shekarar 2023 kamar yadda aka tsara, duk da cewa Najeriya na fama da matsalar tsaro.
Shugaban hukumar farfesa Mahmood Yakubu ne ya tabbatar da hakan a wani taro da suka gudanar a babban birinin tarayya Abuja ranar alhamis.
Inda ya bayyana sun kammala shirye-shiryensu tsaff na gudanar da zaben watanni goma kafin lokaci, kuma ma’aikata kusan miliyan daya ne zasu gudanar da zaben a kananun hukumomi 774 dake Najeriya.