fbpx
Wednesday, June 29
Shadow

Matsalar Tsaro:”kullun da kunci nake kwana”>>Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban kasar Najeriya, Mejo janar Muhammad Buhari ya bayyana cewa gwamnatin tarayya da jami’an tsaro na iya bakin kokarinsu don shawo kan matsalar tsaron kasar.

Inda yace yana kira ga al’ummar Najeriya su saka mutanen dake hannun ‘yan bindiga cikin addu’a a wannan rana ta dimokuradiyya.

Buhari yace kullun da kunci yake kwana yake tashi saboda matsalar tsaron Najeriya, kuma baza suyi kasa a gwiwa ba har sai sun ceto mutanen dake hannun ‘yan bindiga,

Kuma sun gurfanar da miyagun mutanen a gaban kulliyya sannan wa’yanda suka mutu ma zasu bi masu hakkin su.

Leave a Reply

Your email address will not be published.