fbpx
Thursday, August 11
Shadow

Matsalar tsaron Najeriya sai an hada da rokon Allah>>Shugaba Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, Najeriya na bukatar addu’a kamin iya magance matsalar tsaro.

 

Shugaban ya bayyana hakane a wajan addu’ar da aka shirya a Kano dan rokon Allah kan matsalar tsaron da ake fama da ita.

 

Mustapha Babai, karamin Ministan Noma ne ya wakilci shugaba Buhari a wajan taron.

 

Ya bayyana cewa, Najeriya na iya bakin kokarinta wajan magance matsalar tsaron da ake fama dashi.

 

Yace amma duk da kokarin na gwamnati akwai kuma bukatar a roki Allah dan a kawo karshen matsalar tsaron.

Leave a Reply

Your email address will not be published.