Wasu ‘yan ta’addan da ake kyautata zaton ‘yan ISWAP ne sun kashe mutane 16 a kauyen Kurmi karamar hukumar Bama dake jihar Borno.
Kuma a cikin mutanen da suka kashe hadda jami’an soji guda uku a cewar wani mazaunin yankin daya bayyanawa manema labarai na DailyTrust wannan labarin.
Kuma yanzu mutanen yankin da dama sun fara tserewa daga gidajensu a karamar hukumar ta Bama da wannan al’amarin ya faru ranar sati.
Yayin da kuma ‘yan ISWAP din sukayi garkuwa da mutane uku ranar juma’a a karamar hukumar Mungono dake jihar.