fbpx
Friday, December 2
Shadow

MATSALOLIN NIJERIYA: Yadda Buhari Ya Taka Sawun Barawo

Daga Aliyu Ahmad

Wallahi Komawa Ga Allah Ne Kadai Mafita Ga Matsalolin Nijeriya

Ta Yaya Ba Za Mu Tsinci Kanmu Cikin Mawuyacin Halin Da Muke Ciki Ba, Duba Da Yadda A Nijeriya Ne Za Ka Ji Ana Aikata Manyan Laifukan Da Ko A Zamanin Annabawa Ma Ba A Aikata Su Ba

Wasu daga cikin manyan laifukan da ake tafkawa a Nijeriya sun hada da;

*Ka ji an ce ‘Da ya kashe mahifiyarsa ko mahaifinsa don samun abin duniya

*A wulakanta Kur’ani ta hanyar jefa shi cikin najasa

*Uba ya dirkawa ‘yarsa ciki ko kuma ka ji ‘da ya dirkawa uwarsa ciki

*Mace Ta Auri Mace

*Namiji ya auri namiji

*A haifi jarirai a sayar ko matsafa su dafa su ci, ko kuma a kirba su a turmi

*Ga yawaitar ‘yan Daudu da ‘yan Madigo

*Har maza masu yi wa kansu tiyata don komawa jinsin mata akwai a Nijeriya

Karanta wannan  Sharia’r da za’a yi wa Aminu Mohamméd, dolé a yì ta a filí, a fadí Laífin da ya yí, a faɗí laifin da aka yí masa

*An samu wanda ya kashe iyayensa da kannensa mata guda biyu duk a Nijeri

Wannan kadan ne daga cikin wasu manyan laifukan da ake tafkawa a kasar nan, kuma a haka ne muke sa ran za mu ga daidai.

To Wallahi matukar ba mu tuba mun koma ga Allah ba, to babu wani canji da za mu gani saidai mu yi ta shiga mawuyacin hali fiye da wanda muke ciki a yanzu.

Allah ya sa mu gyara dabi’un mu domin mu ga daidai a Nijeriya.

Da wadannan manyan zunuban da ake zabgawa a Nijeriya bana tunanin duk wani shugaba da zai karbi ragamar shugabancin Nijeriya zai iya magance matsalolin da suka yi mata katutu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *