fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Mauricio Pochettino yayi nasarar cin wasan shi na farko a kungiyar PSG bayan daya jagoranci kungiyar ta lallasa Brest daci 3-0

Kungiyar zakarun kasar Faransa ta Paris Saint German ta karbi bakuncin Brest a gasar Ligue 1, inda tayi nasarar lallasa ta daci uku ta hannun Moise Kean, Mauro Icardi da kuma Pablo Serabia.

Sakamakon wasan yasa yanzu maki daya daya kacal tsakanin PSG da Lyon a saman teburin gasar bayan da kungiyar Rennes ta rike Lyon suka raba maki a wasan da  suka tashi daci 2-2.

Sabon kocin PSG, Mauricio Pochettino yayi nasarar cin wasan shi na farko a kungiyar a wasa na biyu daya jagoranta bayan ya raba maki da kungiyar Saint Etienne a wasan shi na farko wanda suka tashi daci 1-1.

Leave a Reply

Your email address will not be published.